Isa ga babban shafi
Najeriya-Tattalin Arziki

An bankado batan Dala biliyan 450 a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sanar da gudanar da binciken asusun hukumominta 33 tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015, inda ta bankado bacewar kudaden da suka kai Dala biliyan 450.

Ministan Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun
Ministan Kudi ta Najeriya Kemi Adeosun
Talla

Minsitan kudin kasar Kemi Adeosun, ta ce tuni suka fara aiki da hukumar EFCC domin gano inda kudaden suka shiga.

Cikin manyan hukumomin da Ministan ta bayyana sun hada da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, hukumar kula da sadarwa, da kuma hukumar tashoshin jiragen sama.

Mallam Nasir Kura, daya ne daga cikin masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ya kuma shaidawa sashin hausa na RFI cewa, abu ne mawuyaci a samu nasarar karbo dukkanin kudaden, kasancewar bincike na tsawon shekaru ne, kuma wasu da ake zargi sun rigamu gidan gaskiya.

Kura a ya ce manyan hanyoyin da suka ragewa gwamnati su ne, tuhumar wadanda aka zargi da suke raye, tare da amfani da ikonta wajen karbe kudaden al’umma da suka yashe.

Mai fafutukar ya kara da cewa, hanya ta gaba kuma ita ce amfani da Diplomasiya wajen karbo kudaden da aka boye a kasashen ketare, bayan tuntunba tsakanin hukumomin kasashen.

A cewar Nasir Kura ta haka ne kawai, za’a iya samun nasarar karbar akalla kashi 60 daga cikin kudaden al’ummar Najeriya da aka karkatar da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.