Isa ga babban shafi
Singapore

An zartar da hukuncin kisa kan dan Najeriya a Singapore

Gwamnatin kasar Singapore ta zartar da hukuncin kisa kan wani dan Najeriya Chijioke Stephen Obioha da kuma dan kasar Malaysia Davendra Supramaniam wadanda aka samu da laifin safarar kwayoyi.

Talla

Hukumar yaki da kwayoyi ta kasar tace an rataye mutanen biyu ne yau a gidan yarin Changi.

Obioha ya yayi tattaki zuwa kasar Singapore ne da niyyar zama kwararren dan wasan kwallon kafa, sai dai a shekara ta 2008, aka kamashi da laifin safarar miyagun kwayoyi mai nauyin kilo 2.6.

A dokar kasar, duk wanda aka kama dauke da miyagun kwayoyi da nauyinsu ya zarta giram 500, zai fuskanci hukunci kisa.

Duk wani kokarin lauyoyi na hana dakatarwar yaci tura, saboda yadda kotu tayi watsi da daukaka karar da sukayi.

Kungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.