Isa ga babban shafi
Najeriya

"A kyale hukumar DSS ta kammala bincikenta kan Alkalai"-Justice Mahmud

A Najeriya da alama har yanzu batun bincikar wasu alkalai da hukumar DSS ke yi na cigaba da kaikawo, kasancewar, Alkalin Alkalan kasar Justice Mahmud Muhammad, yace bai kamata kungiyar lauyoyin Najeriya ta bukaci dakatar da alkalan daga bakin aiki ba.

Talla

Akalin Alkalan ya ce babu bukatar aiwatar da kiran kungiyar lauyoyin kasar, kuma kiran ma tamkar riga malam Masallaci ne kungiyar ta yi, kasancewar hukumar DSS har yanzu bata kammala bincike kan zargin da ake wa alkalan ba.

Har yanzu dai alakalai hudu daga cikin bakwai da jami’an DSS suka kama ranar 7 da kuma 8 ga watan da muke ciki, suna bakin aiki, yayinda Majalisar Shari’ar Najeriya ta dakatar da sauran guda uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.