Isa ga babban shafi
Najeriya

Cin hanci ya yiwa ginshikan tafiyar da gwamnatin Najeriya katutu - Osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce baki dayan manyan ginshikan gwamnatin Najeriya guda uku, wato bangaren Zartarwa, Majalisa da kuma sashin Shari’ah, na fama da katutun cin hanci da rashawa. 

Mataimakin Shugaban Najeriyar Farfesa Yemi Osinbajo
Mataimakin Shugaban Najeriyar Farfesa Yemi Osinbajo
Talla

Yayin da yake jawabi wajen bikin yaye dalibai na Jami’ar Ado Ekiti, Farfesa Osinbajo yace tilas gwamnatin Najeriya ta dauki matakin cire duk wani baragurbin wakilan jama’a daga dukkanin sassan.

Osinbanjo ya kara da cewa, gwamnatin Najeriya zata cigaba da nuna babu sani ba sabo kan duk wadanda aka samu da hannu cikin cin hanci da rashawa.

Makwanni biyu da suka gabata, sumamen da jami’an tsaro na DSS suka kai kan gidajen wasu Alkalai a Najeriya, bisa zargin cin hanci, ya jawo zazzafar muhawara tsakanin al’ummar kasar, inda da dama ke goyon bayan hakan.

Sai dai a bangare guda Majalisar sashin shari’ah na kasar, ya ce matakin ya sabawa ka’ida, yayinda ita kuma kungiyar lauyoyi ta kasar ke goyon bayan matakin tare da yin kira da a dakatar da lauyoyin, har sai sun wanke kansu daga zargi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.