Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa kan Iyalan Marigayi Tafawa Balewa

Wallafawa ranar:

Ranar 1 ga watan Oktoba, ta kasance mai girma a tarihin Nigeria, kasancewa a ranar kasar ta samu ‘yancin mulkin kai daga kasar Ingila, inda a gobe ake cika shekaru 56 da samun ‘yancin.

Talla

Daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar samar wa kasar wannan ‘yanci, akwai Alhaji Abubakar Tafawa Balewa, wanda ya rike mukamin Firaministan farko a kasar.

Shekaru kusan 50 bayan kisan gillar da aka yi wa marigayi Tafawa Balewa, ko yaya yanayin rayuwar iyalan da ya bari ?

Muhammad Ibrahim Bauchi ya zanta da daya daga cikin ‘ya’yansa wacce yanzu ke rike da mukamin Shugabar Hukumar Yaki da Jahilci a jihar Bauchi, Hajia Yelwa Abubakar Tafawa Balewa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.