Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta ci gaba a cikin shekaru 56

A yayin da Najeriya ke cika shekaru 56 da samun ‘yanci daga turawan mulkin mallaka a gobe Asabar, tsohon kakakin Sardaunan Sokkoto, Ahmdu Bello ya mayar da martani kan masu caccakar Najeriya.

Firaministan Najeriya a Jamhuriyya ta farko Marigayi Sir Abubakar Tafawa balewa
Firaministan Najeriya a Jamhuriyya ta farko Marigayi Sir Abubakar Tafawa balewa
Talla

Malam Garba Gumel wanda shi ne tsohon jami’in watsa labarai a karkashin Sardauna, ya bayyana masu fadin cewa, kasar ba ta samu ci gaba ba a matsayin marasa cikakken ilimin tarihin Najeriya.

Tsohon jami’in ya ce, yana dariya a duk lokacin da wani marubuci ya ce, kasar ba ta ci gaba ba tun bayan samun ‘yanci.

“Tsoffin shugabanninmu da suka jajirce wajen karban mana ‘yancin za su yi alfahari da mu a duk in da suke a yanzu.” in ji Gumel.

Gumel ya bayar da misalin ci gaban da kasar ta samu, in da ya ce, makarantun sakandare guda hudu ne kacal ake da su a lardin Kano na wancan lokacin, yayin da ake da guda biyar a Kaduna.

Sannan kuma wuraren da ke da wutar lantarki a Kano kalilan ne, da suka hada da birnin Kano da Hadeija da Gumel da Kazaure da Dawakin Tofa.

“ To a yanzu, tashoshin wutar lantarki guda nawa ne a jihohin Kano da Jigawa kadai ba tare da mun kidaya wadanda ake da su a sauran jihohin kasar 36 da kuma kanta Abuja ba?” In ji Gumel.

Har ila yau, tsohon kakakin na Sardauna ya lura cewa, an samu gagarumin ci gaba a fannoni da dama da suka hada da ilimi da lafiya da hanyoyi da sadarwa da zirga-zirgar abawan hawa da sauransu.

Daga karshe dai, tsohon ma’aikacin gwamnatin ya jinjina wa Sardanan Sokkoto da Malam Aminu Kano da Sir Abubakar Tafawa Balewa da Nnamdi Azikwe da Cif Obafemi Awolowo da kuma Cif Chris Okotie-Eboh kan rawar da suka taka wajen ‘yanto Najeriya daga hannun turawan mulkin mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.