Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun tarwatsa sabon sansanin Boko Haram

Rundunar sojin sama ta Najeriya, ta ce a harin da ta kai daren ranar Litinin, ta yi nasarar lalata sabon sansanin da mayakan Boko Haram suka kafa, a yankin da ke tsakanin Malam Fatori da Kangarwa a arewacin jihar Borno.

Sojin Najeriya suna samun nasara kan Boko Haram
Sojin Najeriya suna samun nasara kan Boko Haram AFP
Talla

Kakakin rundunar sojin saman, Kaftin Ayodele Famuyiwa, ya ce sabon sansanin bashi da nisa da sansanin da rundunar ta kaiwa hari a ranar 20 ga watan Agustan da muke ciki, wanda tayi nasarar raunata jiga jigan mayakan na Boko Haram da kuma kashe wasunsu da dama.

Famuyiwa ya kara da cewa sojin saman Najeriyar, sun kuma samu nasarar dakile awni hari da kungiyar Boko Haram din ta shirya kaiwa kan bataliyar soja ta 153 da ke Ala Lumshe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.