Isa ga babban shafi
MDD-Najeriya

MDD ta bukaci Najeriya ta dau matakan gaggawa kan 'yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Gwamnatin Najeriya da kungiyoyin kasashen duniya da su dauki matakan gaggawa dan kare lafiyar dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajen su a Yankin Arewa maso Gabashin kasar.

'Yan gudun hijira sakamakon Boko Haram na cikin wani yanayi a Najeriya
'Yan gudun hijira sakamakon Boko Haram na cikin wani yanayi a Najeriya AFP PHOTO/OLATUNJI OMIRIN
Talla

Wakilin Majaisar Chaloka Beyani yayi kiran bayan ya ziyarci yankunan na kwanaki 4 inda ya bayyana abinda idansa ya gani a matsayin gagarumin tashin hankali.

Chaloka Beyani da ya kwashe kwanaki hudu yana karade sassan arewa maso gabashin Najeriya dan ganin halin da jama’ar yankin ke ciki, musamman ‘yan gudun hijira yace yanzu ne duniya ta fara ganin zahiri kan halin da wadannan dubban mutanen da rikicin ya raba da mastugunin su ke ciki.

Jami’in yace da yawa yunwa da rashin abinci mai gina jiki ya yiwa yara da dama illa, kana ga kaduwar da suka yin a halin da suka shiga na tashin hankali.

Beyani yace akalla mutane sama da miliyan biyu da rabi rikicin na Boko Haram ya raba da muhallin su a Ynakin, saboda haka babu dailin da za a kauda kai wajen ceto rayuwar wadanann mutane wajen samar musu abinci mai gina jiki, matsuguna, kula da lafiyar su, tsabtacacen ruwan sha da kuma sauran kayan more rayuwa.

Jami’in ya kuma ce akasarin mutanen da rikicin ya shafa amma basa zama a sansanin da aka tanadar, basa samun taimakon da ya dace, inda ya bada shawarar nemo su domin ganin suma an tallafa musu.

A karshe yayi kiran samarwa yan gudun hijirar tsaron da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.