Isa ga babban shafi
Najeriya

Kano: ‘Yan hisbah na fuskantar shari'a

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wasu jami'an hukumar hisbah Uku gaban wata kotun shari'a dake birnin Kano bisa zargin su da lakadawa wasu 'yan jaridu dukan tsiya.

An gurfanar da 'yan hisbah gaban kotu bayan cin zarafin 'yan jaridu
An gurfanar da 'yan hisbah gaban kotu bayan cin zarafin 'yan jaridu
Talla

Lokacin zaman kotun dai lauyan wadanda ake kara Barirster Nabahani, ya bukaci da ayi sulhu, sai dai lauyan masu kara Barister Abdu Bulama Bukarti ya amince amma bisa tsauraran sharuda, abunda yasa kotun ta dage zaman sai zuwa ranar 28 ga watan Satumba.

A ranar lahadin karshen mako ne dai jami'an hisbar suka ci zarafin ‘yan jaridun biyu dake aiki da gidan radiyon Express a birnin Kano, lokacin da suke kokarin daukar wani rahoto a filin baje koli, abun da yasa ‘yan sanda suka kame ‘yan hisbar tare da gurfanar dasu gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.