Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun yi ikirarin raunana Shekau a Sambisa

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kashe wasu daga cikin manyan 'ya'yan kungiyar Boko Haram a wani harin sama da suka kai kauyen Tale dake Gombale a dajin Sambisa.

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Sanarwar da kakakin sojin kasar Kanar Sani Usman kukasheka ya sanyawa hannu ta nuna cewar cikin wadanda aka tababtar da mutuwar su harda Abubakar mubi, Malam Nuhu da malam Hamman, yayin da kuma aka sanar da raunana Abubakar Shekau.

Rundunar ta sanar da aniyar ta na ci gaba da bude wuta duk da bukatar kungiyar Boko Haram na musayar ‘yan kungiyar su da 'Yan matan Chibok.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.