Isa ga babban shafi
Najeriya

Kashi 40% na yara kanana a Najeriya basa zuwa makaranta.

Yayin da ake bikin tunawa da ranar kula da yawan al’umma ta duniya, alkalumma na nuni da cewa Najeriya na sahun gaba cikin kasashen da suke da yara kanana da basa iya zuwa makaranta.

Malam Nasir El Rufa'i Gwamnan jihar Kaduna
Malam Nasir El Rufa'i Gwamnan jihar Kaduna via El rufa'is facebook page
Talla

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, wanda ya bayyana hakan a wajen wani taro da ma’aikatar kasafin kudin jihar ta shirya, ya ce arewacin Najeriya ne kan gaba wajen samun yawan yara da basa iya zuwa makaranta.

A cewar El-Rufa’i kimanin kashi 40% na yara a Najeriya basa halartar makarantun firamare, musamman ‘ya’ya mata, kuma arewacin kasar ne ke da kaso mafi tsoka.

A cewarsa kama ta yayi ace jihohin arewacin kasar su maida hankali wajen bawa ilimin kananan yara muhimmanci musamman ‘ya’ya mata ta hanyar samar da ilimin kyauta.

Gwamnatocin yankin arewacin Najeriyar dai sun sha daukar alkawuran shawo kan matsalar rashin halartar makarantun firamare a bagaren kananan yara, matsalar da har yanzu ta ke ciwa al’ummar yankin tuwo a kwarya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.