Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan majalisar Najeriya sun bukaci a binciki Dogara

Wasu mambobin majalisar wakilan Najeriya sun bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su tsoma baki kan zargin da ake yi wa kusoshin majalisar na kokarin shigar da cuwa-cuwa a kasafin kudin shekara ta 2016.

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Hon. Yakubu Dogara
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Hon. Yakubu Dogara bellanaija.com
Talla

‘Yan majalisar wadanda suka gabatar da kansu a karkashin wata sabuwar kungiya mai suna “Transparency Group”, na bukatar a binciki shugabansu, Yakubu Dogara da mataimakinsa Yusuf Lasun da mai tsawatarwar majalisar, Ado Doguwa da kuma shugaban masu rinjaye Leo Ogor kan zargin shigar da ayyukan jabu a cikin kasasfin.

Kungiyar wadda ke da mambobi fiye da 100 daga shiyoyin kasar shida, ta ce, zargin ya shafi kusoshin majalisar ne kadai amma ba daukacin ‘yan majalisar ba.

Har wa yau, kungiyar ta tsame kanta daga jawabin da shugaban kwamitin yada labarai na majalaisar Abdulrazak Namdas ya yi wa manema labarai a ranar Talata kan wannan batu.

Wannan dai na zuwa ne bayan Dogara ya bai wa Abdulmumin Jibin, tsohon shugaban kwamitin kula da kasafin kudi, wa’adin kwanaki bakwai da ya janye zargin da ya yada ko kuma ya fusaknci fishin shari’a.

Sai dai Hon. Jibrin ya tsaya kan bakarsa tare da fadin cewa, a shirye yake ya hadu da Dogara a kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.