Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana shirin kara kudin wutar lantarki a Najeriya

Kamfanonin da ke rarraba wutar lantarki a Najeriya na shirin kara kashi 100 na kudin wutar da al’ummar kasar ke biya.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki na Najeriya na shirin kara kudin wuta ga al'ummar kasar
Kamfanonin rarraba wutar lantarki na Najeriya na shirin kara kudin wuta ga al'ummar kasar REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

A cikin watan Fabairun da ya gabata ne kamfanonin suka kara kashi 45 cikin 100 na kudin, abinda ya haifar da cece-kuce a duk fadin kasar.

Kamfanonin sun aika da takarda zuwa ga hukumar da ke kula da wutar lantarki ta Najeriya, inda suka bukaci a kara kudin zuwa Naira 50 a kan kowani kilowatt guda daga Naira 24 ga masu amfani da wutar a gidaje.

Sai dai tuni ‘yan kasar suka fara nuna adawa da shirin, inda Darekta Janar na kungiyar masu masana’antu a kasar Remi Ogunmefun ya ce, suma sun aike da takarda zuwa ga hukumar kula da wutar, inda suka bayyana rashin amincewarsu da matakin.

‘Yan Najeriya dai na kokawa da rashin samun wadatacciyar wutar lantarki duk da karin da aka yi musu watanni shida da suka gabata.

A bangare guda, matsalar rashin wuta ce ta yi sanadiyar durkushewar kamfanonin kasar da dama yayin da wasu kuma, suka koma kasashen ketare domin ci gaba da harkokinsu.

Masharhanta kan tattalin arziki sun ce ficewar kamfanonin daga Najeriya ta haifar da nakasu ga tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.