Isa ga babban shafi
Najeriya

PENGASSAN ta ki zama da gwamnatin Najeriya

Shugabannin kungiyar manyan ma’aikatan man fetir da samar da iskar gas ta Najeriya PENGASSAN, sun ce ba za su tattauna da gwamnatin kasar ba a yau Jumma’a kamar yadda aka shirya a baya.

Ana fargabar rashin jituwa tsakanin gwamnati da ma'aikatan man ka iya haifar da illoli game da samar da man fetir a kasar
Ana fargabar rashin jituwa tsakanin gwamnati da ma'aikatan man ka iya haifar da illoli game da samar da man fetir a kasar AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu dalilai amma za ta zauna da gwamnatin ta tarayya a ranar Litinin mai zuwa.

Wannan na zuwa ne bayan mambobin kungiyar sun shiga yajin aiki a jiya Alhamis, inda tuni wasu daga cikin su suka fara janye kayayyakinsu daga gabar ruwa da sauran wuraren da suke lodi.

Kungiyar ta fara yajin aikin ne duk da kokarin da ministan kwadago da samar da ayyukan yin a kasar, Sanata Chris Ngige ya yi don ganin ya dakatar da su.

Sabon yajin aikin na zuwa ne bayan ma’aikatan sun yi korafin cewa, gwamnatin ta gaza biya musu bukatunsu duk da cewa sun tattauna da da gwamnati har sau biyu a cikin watan jiya.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.