Yau ne Fulani za su fice daga kudancin Najeriya
Yau ne wa’adin da matasan Igbo suka bai wa Fulani makiyaya da ke kudu maso gabashin Najeriya da su fice daga yankin ke cika, ko kuma su yi amfani da karfi wajen korar su.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Matasan sun bayar da wa'adin ne karkashin kungiyar Ohanaeze ta kabilar Igbo kuma daukan matakin ya biyo bayan zargin Fulanin da hallaka 'yan kabilar Igbo sama da 40 a jihar Enugu, kamar yadda shuagban matasan Mazi Obinna Achuoye ya bayyana.
Shugabannin Fulani sun musanta zargin cewa, Fulani makiyaya ne suka kaddamar da harin.
Bayan wani taro da suka yi a jihar Kaduna, gwamnonin yankin Arewacin kasar sun bayyana bacin ransu kan yadda ake cin zarafin Fulanin, maimakon hukunta wadanda suka aikata laifi.
Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya yi Allah-wadai kan yadda ake alakanta rikicin Fulani da siyasa a Najeriya.
Kashim Shettima kan rikicin Fulani
Shugabannin kabilar Igbo na cewa, rikicin Fulani ya tirsasa wa mata da kananan yara ficewa daga gidajensu yayin da rahotanni ke cewa, tuni wasu daga cikin Fulani da Hausawa suka fara ficewa daga jihar Enugu, inda aka samu rikici na baya-bayan nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu