Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya sun kosa da mulkin Buhari- NLC

Kungiyar kwadago ta NLC da kungiyar kwararrun kungiyoyi ta TUC sun ce, ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya sun fara kosawa da mulkin shugaban kasar Muhammadu Buhari saboda ba su ga wata alamar canji ba kamar yadda gwamnatin APC ke ikirari.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Kungiyoyin biyu sun bayyana haka ne a yayin gudabnar da bikin ranar ma’aikta ta duniya a biranen Abuja da Legas a jiya Lahadi.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa ma’aikata da ‘yan Najeriya cewa, gwamnatinsa na kokarin magance dukkanin matsalolin da ke addabar Najeriya da suka hada da na tattalin arziki.

Sai dai kungiyoyin sun hada kai wajen yin Allah wadai da talaucin da ake ci gaba da fama da shi da kuma rashin aikin yi, har ma da matsalar tsaro da rashin wadatacciyar wutar lantarki da matsalar karancin man fetur.

Dukkanin kungiyoyin sun yi gangami ne a biranen Abuja da Legas, inda suka yi magana da yawu guda kuma akan abu guda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.