Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya lallashi 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar da su kara hakuri saboda halin kuncin da suke ciki, yayin da ya bayar da umarnin sakin Tan dubu 10 na abinci daga rumbun adana kayan abinci na kasa, a wani mataki na samar da sassauci ga al’umma.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS
Talla

Shugaba Buhari ya ce, nan kusa 'yan Najeriya za su fara ganin tasirin canjin da suka zaba a dukkanin sassan kasar.

Wata sanarwa da fadar Buhari ta fitar ta ce, gwamnatin tarayya ta yi asarar Naira tiriliyan 9 saboda rikicin Boko Haram, abinda da ya kara tsananta matsalar tattalin arzikin da kasar ke ciki.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da jerin shirye-shiryenta don inganta rayuwar al’umma, da suka hada da  shirin bai wa marasa galihu tallafin Naira dubu 5 a duk  karshen wata, wanda ta ce, nan kusa za a fara aiwatarwa.

Gwamnatin dai na bukatar ‘yan Najeriya su fahimci cewa, ta gaji tarin matsaloli daga tsohuwar gwamnatin da ta shude.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.