Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Huldar Najeriya da China ta fuskar tattalin arziki

Wallafawa ranar:

Yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kawo karshen ziyarsa da ya kai a kasar China, yanzu haka masana tsarin tattalin arziki na ci gaba bayyana mahangarsu a game da alfanun da ke tattare da wannan ziyara ta kusan mako daya.Wani abu da ya fi daukar hankulan jama’a a nan shi ne sanarwar da aka bayar cewa, Najeriya za ta fara amfani da takardar kudin kasar China wato Yuan a matsayin asusun ajiya, sabanin yadda kasar ta fi dogara a dalar Amurka domin yin wannan ajiya.Kasimu Garba Kurfi masani tsarin tattalin arziki a babbar kasuwar hannayen jarin Najeriya da ke birni Lagos, ya bayyana amfanin hakan a wata zantawa da ta hada shi da sashen hausa na gidan rediyon faransa rfi hausa. 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari statehouse
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.