Isa ga babban shafi
Najeriya-Saudiya

Najeriya zata shiga cikin rundunar kawancen Musulunci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar zata shiga cikin rundunar hadin gwiwar kasashen Musulmi karkashin Saudi Arabia da ke fada da ta’addanci.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A wata hira da tashar talabijin ta Al jazeerah shugaba Buhari ya ce Najeriya na cikin bala’in fada da ‘yan ta’adda da ke ikirarin musulunci, inda ya bada misali da kungiyar Boko haram da ta yi sanadin mutuwar mutane dubu ashirin tun daga shekarar 2009.

A lokacin ziyarar sa a kasar Saudiya shugaba Buhari ya ce ko baza su shiga kane-kane cikin rundunar ba, to dai suna goyon baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.