NUPENG da PENGASSAN na adawa da matakin raba NNPC
Kungiyoyin ma’aikatan man fetir a Najeriya wato NUPENG da PENGASSAN sun yi watsi da shirin rarraba babban kamfanin mai na NNPC zuwa rassa har 30, saboda fargaba cewar ma’aikata da dama a kamfanin zasu rasa ayyukansu.
Wallafawa ranar:
A ranar Laraba ne dai ministan kasa na man fetire Dr Ibe Kachikwu ya bayyana matakin kasa kamfanin NNPC har rassa 30.
Kuma ministan yace nan da mako guda ne suke fatar aiwatar da sauyin a kamfanin na NNPC.
Amma shugaban kungiyar PENGASSAN ta manyan ma’aikatan mai a Najeriya ya ce ba su goyon bayan matakin na raba NNPC, a cewar shugaban kungiyar Emmanuel Ojugbana a yanke shawarar raba NNPC ne ba tare da saninsu ba.
Sai dai yace zasu gana domin daukar matakin da ya dace don suna son asan yadda matakin zai shafi ma’aikata.
Tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari mulki ne ake ta duba batun sake fasalta kamfanin NNPC dake fama da matsalar rashawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu