Isa ga babban shafi
Najeriya-Qatar

Buhari ya koka kan rashin dai-daituwar farashin man fetur a duniya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya da ta dauki matakin dai-daita farashin inda yake cewa yadda ake sayar da man a yau ba abinda za’a amince da shi ba ne.

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Buhari ya shaidawa Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hammad al Thani cewar yadda farashin man yake a yau ba abune da kasashen dake hakoshi za su yi zuba ido ba ne.

Shugaban na Najeriya ya bukaci hadin kai tsakanin kasashen dake cikin kungiyar OPEC da wadanda basa ciki dan daidaita farashin a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.