Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan matan Chibok ba za su dawo ba- Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya haifar da shakku dangane da dawowar ‘yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta yi awon gaba da su kusan shekaru biyu a jihar Borno.

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo. AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

A lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wani taro da kungiyar malaman jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife ta shirya a jiya jumma’a, Obasanjo ya ce, duk wanda ya ce ‘yan matan za su dawo, to karyar kawai ya ke fadi.

Obasanjo ya caccaki tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan kan rashin daukan matakin ceto ‘yan matan a ranar da aka sace su duk da kiraye kirayen da aka yi ta yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.