Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Kogi: PDP ta bukaci Malami da ya yi murabus

Jam’iyyar PDP ta Najeriya ta bukaci mai shigar da kara na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da ya yi murabus daga mukaminsa bayan ta zarge shi da matsa wa hukumar zaben kasar, INEC.

Tambarin jam'iyyar PDP
Tambarin jam'iyyar PDP
Talla

PDP na zargin Malami da takura wa INEC har ta yanke hukuncin da ya saba wa doka bayan ta bai wa jam’iyar APC damar tsayar da sabon dan takarar da zai wakilce ta a zaben gwamnan jihar Kogi da ake sa ran kammalawa a ranar 5 ga watan gobe.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin PDP Olisa Metuh, ta bayyana cewa, jam’iyyar ta yi matukar mamaki kan yadda INEC ta yi sake har APC  ta juya ta yadda ta ke so bayan ta bi umarnin da mai shigar da karar ya bayar na sauya dan takara a dai-dai lokacin da ake cikin tsakiyar zaben.

A jiya ne dai hukumar zaben ta fitar da wata sanawar, inda ta bukaci APC da ta fitar da wanda zai wakilce ta a zaben jihar ta Kogi sakamakon rasuwar tsohon dan takararta Prince Abubakar Audu wanda ya rasu gabanin a kammala zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.