Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sandan sun cafke dilalan tabar wiwi a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar kano da ke arewacin Najeriya da hadin gwiwar ‘yan kungiyar tsaro ta vigilante, ta kama wasu dilolin tabar wiwi 3, ciki har da wata tsohuwa mai shekaru 70, da ake zargi da bada gidan haya ga dilolin tabar wiwin a unguwar ja'en dake birnin kano.A lokacin da ya ke gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai kwamishinan ‘yan sanda jihar Kano, Muhammad Musa katsina ya ce an kama tabar wiwi Mai nauyin kilogram dubu 24 da kudinta ya zarce naira miliyan sittin. Wakilinmu Abubakar Isah Dandago na dauke da rahoto akai. 

Ana fama da matsalar kwankwadan miyagun kwayoyi tsakanin matasa a Najeriya.
Ana fama da matsalar kwankwadan miyagun kwayoyi tsakanin matasa a Najeriya. Reuters/Chaiwat Subprasom
Talla

03:18

'Yan sandan sun cafke dilalan tabar wiwi a Kano

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.