Isa ga babban shafi
Najeriya

Saraki ya bayyana sunayen Ministocin Najeriya

Shugaban Majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya bayyana sunayen Mutane 21 da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aikewa Majalisar makon daya gabata domin na da su a Matsayin Ministoci.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sunanyen da Shugaban ya aike sun hada da mai Magana da yawun Jam’iyyar APC Lai Mohammed, da wasu tsoffin gwamnoni wato Chibuike Amaechi da Babatunde Fashola.

A cikin jerin sunanye kuma akwai Tsohon babban hafsan sojin kasa Janar Abdurrahman Dambazzau, tsohuwar ‘yar takarar gwamnan Taraba Aisha Alhassa, da Adebayo Shittu tsohon Senata da Udo Udoma da kuma Ibrahim Jibril.

Sauran kuma akwai tsohon Sanata Suleiman Adamu, Chris Nigige da Kemi Adeosun da kuma Ahmed Ibeto da Hadi Sirika, kana akwai tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Cif Audu Ogbeh wanda kuma ya taba rike mukamin Ministan sadarwa a zamanin mulkin Shugaba Shehu Shagari mai shekaru 68.

Shima tsohon gwamnan Anambra Ogbonnaya Onu na cikin wadanda aka fitar da sunansu, sai shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC Ibeh Kachikwu, Amina Muhammed da Solomon Dalong daga jihar Filato, Suleaman Adamu da tsohon gwamna Ekiti Kayode Fayemi.

Shugaban Majalisar dattawan Bukola Saraki ya ce daga ranar 13 ga watan Okotoba Majalissa za ta soma tantance ministocin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.