Isa ga babban shafi
Najeriya

An cafke Diezani a London

Rahotanni daga Britaniya sun tabbatar da cewa jami’an tsaro kasar sun cafke tsohuwar ministar albarkatun mai Najeriya Diezani Alison-Madueke a birnin London.

Tsohuwar Ministar albarkatun mai a Najeriya Diezani Allison-Madueke
Tsohuwar Ministar albarkatun mai a Najeriya Diezani Allison-Madueke AFP / Wole Emmanuel
Talla

Mai Magana da yawun ofishin jakadancin Birtaniya a kasar Joseph Abuku ya tabbatar da cewa hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a London sun damke Madueke tare da wasu mutane hudu dangane da zargin rashawa a safiyar yau Juma'a a kasar.

Yayin da wasu majiyoyi ke cewa Jami'an Hukumar EFCC na Najeriya sun gudanar da bincike a gidanta dake Abuja a yau.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a jawabinsa na cika kasar shekaru 55 da Yanci kai ya jadada matsayin gwamnatinsa na yaki da cin hanci da rashawa musamman a bangaren man fetur na kasar.

Buhari wanda ya  bayyana kansa a matsayin wanda zai jagoranci ma'aikatar man Feturi, ya ce gwamnatinsa na samun bayanai akan kudaden da aka sace a ma'aikatar, kuma nan bada dadewa ba za a fara hukunta wadanda ake zargi.

Tun gabanin rantsar da Shugaba Buhari a karagar Mulki, Alison-Madueke ta fice daga kasar zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.