Isa ga babban shafi
Najeriya

Bama bamai sun hallaka mutane a Maiduguri

Rohotanni daga garin Maiduguri na jihar Borno dake Najeriya sun ce wasu jerin bama bamai 4 sun tashi a daren jiya a harin kunar bakin wake inda suka hallaka mutane da dama a Ajilari.

Bako Haram ta kaddamar da hare hare a Maiduguri.
Bako Haram ta kaddamar da hare hare a Maiduguri. AFP PHOTO
Talla

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da harin wanda ta ce ya hallaka mutane 14 da kuma jikkata wasu 39 kamar yadda Daraktan yada labaranta Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya sanar.

Ko a watan jiya sai da maharan kungiyar Boko Haram suka hallaka mutane sama da 100 a irin wannan harin.

A bangare guda, rundunar Sojin ta ce mutane 80 daga mayakan na Boko Haram sun mika kansu ga rundunar dake yaki a Bama dake  Jihar Borno yayin da Kanar Usman ya ce kofa a bude take ga mayakan su mika kansu ko kuma su gamu da fushin soji.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.