Alhazan Najeriya da suka mutu a Saudiya sun karu
Hukumar Alhazan Najeriya ta sanar da karin adadin alhazan da suka mutu zuwa 64 sakamakon turmutsitsin da ya auku a Mina wajen Jifan shedan a makon da ya gabata.Kana akwai mutane 244 da ba a san inda suke ba har yanzu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kakakin hukumar Malam Uba Mana wanda ya bada Sanarwa a garin Makkah na kasar Saudiya ya ce izuwa yanzu bayan wadanda suka mutu akwai wasu 71 da ke kwance a Asibiti sakamakon raunin da suka samu
Shima dai Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi Hukumar Alhazan kasar ta tabbatar da cewa lallai an san halin da dukkan alhazai suke ciki.
Umarni Buhari ya biyo bayan rashi gamsassun bayanai ne daga hukumomin Najeriya game da mamata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu