Isa ga babban shafi
Saudi

Alhazan Najeriya 54 sun rasu a aikin Hajji

Hukumar Alhazan Najeriya ta fitar da kididdigar adadin Alhazan da suka rasu bayan hadarin da ya faru a ranar alhamis da ta gabata akan hanyarsu ta zuwa wajen jifan shaidan, inda ta ce Alhazan Najeria 54 ne suka rigamu gidan gaskiya

Mutane 769 suka rasu a wajen jifan shaidan a Saudiya
Mutane 769 suka rasu a wajen jifan shaidan a Saudiya REUTERS/Stringer
Talla

Hukumar ta bayyana haka ne a wani taro da ta yi a cikin daren jiya a garin Makka dake Kasar Saudiya.

Hukumar ta kara da cewa Alhazan da suka rasu sun fito ne daga jihohi 15 na Najeriya wato Bauchi, Borno, Cross rivers, Jigawa, Kano, Katsina, da kuma Kebbi, sauran kuwa su ne Nassarawa, Niger, Ondo, Ogun, Sokoto, Taraba, Yobe da kuma jihar Zamfara

Shugaban hukumar Alhazan Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad ya ce, Alhazai 77 na Kasar sun samu raunuka a tirmutistsin yayin da  wasu suka bata.

Tuni dai aka kafa wani kwamiti domin bincike game da Alhazan da suka bata tare da tabbatar da adadinsu.

Kawo yanzu dai hukumomin Kasar Saudiya sun tabbatar da mutuwar Mahajjata 769  cikin kimanin Miliyan 2 da suka isa Kasar domin aikin hajji na bana, kuma 'Yan Kasar  Iran ne hadarin ya fi ritsawa da su, inda Alhazan Kasar 144 suka rigamu gidan gaskiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.