Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kwato Gamboru Ngala

Sojojin Najeriya sun kwato garin Gamboru Ngala dake a Jihar Borno daga hannun Mayakan Boko Haram, Garin da ke kusa da kan iyakan kasar da Kamaru, kamar yadda Kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Sani Kukasheka ya sanar, ya kuma kara da cewa  a ranar Talata ne Sojin suka kwato garin.

Soji a garin Gamboru Ngala
Soji a garin Gamboru Ngala REUTERS/Stringer
Talla

Rundunar Sojin da ke cike da farin ciki sun watsa jam’ian tsaro a duk sassan garin domin kara kwantar da hankulan jama'a tare da tabbatar da tsaro.

Tun a watan Agustan bara ne mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai kazamin hari a barikin soji da ke garin kafin daga bisani su kwace ikon garin na Gamboru Ngala baki daya.

Daga baya dai dakarun kasar Chadi sun fatattaki mayakan bayan sun kai samame a mabuyar mayakan a watan Febrairun da ta gabata.

Sai dai kuma mayakan sun mayar da martani inda suka kaddamar da wani sabon hari tare da kwace garin, Gamboru Ngala dai ya ci gaba da kasancewa a karkashin ikon mayakan na Boko Haram kafin rundunar Sojin Najeriya ta ci karfin mayakan tare da kwace ikon garin da ya matukar tafka asarar rayuka da dukiya sakamakon ayyukan Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.