Isa ga babban shafi
Najeriya

Tagwayen bama-bamai sun ta shi a tsakiyar kasuwar Gombe

Wani harin tagwayen bama-bamai da aka kai a kasuwar gombe da ke arewacin Najeriya a dai-dai lokacin da jama;a ke hada-hada cinikin Sallah ya yi ajali mutane da dama tare da barin wasu a cikin munannar rauninka

REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahotanin sun ce bam din farko ya tashi ne a inda ake cin kasuwan takalma, kafin daga bisa na biyu ya sake tashi a wajen shagon wasu 'yan china.

Badamasi Amin wani mai siyar da kayayaki a kasuwar ya shaidawa Kamfanin dilanci Labaran Faransa AFP cewa alkallumar mutane da harin ya yi wa illa na da yawa.

Har yanzu dai babu wanda ya dau alhakin wannan harin, to sai dai Jihohi irin su Gombe da Borno da Yobe da Kuma Adamawa na yawan fuskanta hare-haren mayakan Boko Haram wanda a yanzu ya yi sanadi mutuwar mutane sama da dubu 15 daga shekarar 2009 kawo yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.