Isa ga babban shafi
Najeriya

Rikicin zaben Shugaban majalisar dattijan Najeriya ya kusa karewa

Da alama dambarwar siyasar data kunno kai jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya na gab da kawo karshe, bayan da uwar jam’iyyar ta bayyana amincewa da Sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar Dattijan kasar.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kafafen yada labarun kasar sun rawaito shugaban jam’iyyar na kasa Cif John Odigie-Oyegun, na cewa tunda Sanatocin sun zabi Saraki a matsayin shugabansu, a shirye jam’iyyar take ta amince da hakan.
A baya uwar jam’iyyar ta APC ta sa kafa tayi fatali da zaben da wasu sanatocin kasar suka yiwa Saraki a matsayin shugaban majalisar, maimakon Sanata Ahmed Lawan da jiga jigan jam’iyyar suka so a zaba.
Bayan zaben, uwar jam’iyyar ta APC ta kuma yi barazanar sanya wa Sanata Saraki takunkumi, saboda kunnen kashin da yayi wa umarnin jam’iyyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.