Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Google zai taimakawa Masana’antun Najeriya a Android

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa da ke yin nazari tare da tattauna batutuwan da suka shafi ilimin kimiya da fasaha a duniya, a wannan makon ya tattauna ne game da wani sabon shiri a Najeriya na bunkasa ayyukan fasaha ta hanyar amfani da kasuwar Android mallakin kamfanin Google.

Shirin Google na taimakawa Masana'antun Najeriya a Masarrafar Android
Shirin Google na taimakawa Masana'antun Najeriya a Masarrafar Android RfI Hausa/Awwal
Talla

Lura da wadatuwar Android a tsakanin al’umma a zamanin ci gaban fasaha a yanzu, kamfanin Google ya bullo da wani shiri na ba kamfanoni da ‘Yan kasuwa hanyar samar da manhajarsu a kasuwar Android domin bunkasar ayyukansu a kyauta.

A makon jiya ne aka kaddamar da sabon shirin a babbar kwalejein kamiya da fasaha a Bauchi, wadda ita ce cibiya ta farko da aka bude a arewacin Najeriya, bayan ta Lagos da Fatakwal.

Wata kungiya ce ke tafiyar da jagorancin shirin da ake kira Google Developer Group.

Fito da tsarin wata dama ce Google ya ba masana’antu ta yadda za su shiga a dama da su a bajakolin kasuwar duniya a Intanet.

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna da Jagoran shirin Umar Sale Tsohon malami a Jami’ar Tafawa Balewa da ke Bauchi da kuma wasu da suka fara cin gajiyar shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.