Isa ga babban shafi
Najeriya

Morocco ta janye Jakadanta daga Najeriya

Hukumomi a kasra Maroko, sun bayyana janye Jakadansu a Najeriya, bayan wata takaddamar da ta taso tsakanin kassahen biyu, mai alaka da harkokin Diplomasiyya

Mohamed VI, king of Morocco
Mohamed VI, king of Morocco Reuters
Talla

Yanzu haka an shiga takun-saka a fagen diplomasiyya tsakanin Najeriya da Maroko, inda Maroko ta janye jakadanta daga Abuja kai tsaye.

Majiyoyin sun ce sabanin ya samo asali ne bayan da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar da cewa an yi wata tattaunawa ta wayar Tarho tsakani Goodluck Jonathan na Najeriya, da kuma sarki Mohammad na 6 na kasar Maroko, yayin da fadar sarkin ta Maroko ta musanta haka.

Majiyoyi a kusa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya sun bayyana cewa tun a cikin makon da ya gabata ne hukumomin kasar ta Maroko suka soma nuna wa Najeriya bacin ransu dangane da wasu bayanai da ke cewa an yi tattaunawa ta wayar tarho tsakanin mutanen biyu, kafin daga bisani shafin yada labarai na ma’aikatar harkokin wajen Maroko ya musanta cewa an yi tattaunawar.

Bayanan suka ci gaba da cewa, sarkin na Maroko ya ki amincewa da yin tattaunawar ne da shugaba Jonathan saboda yiyuwar yin amfani da hakan domin cimma wasu manufofi na Siyasa, lura da cewa Najeriya na a cikin hali na yakin neman zabe ne.

To sai dai duk da cewa Sarki Mohammad na shida bai amince da yin tattaunawar ba, sai ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ci gaba da cewa mutanen biyu sun tattauna, kuma ga alama wannan ne ya fusata hukumomin na Maroko har ma suka janye jakadansu daga Najeriya.

Duk da cewa Maroko ta kira jakadanta ne domin tattaunawa, kawo yanzu babban abin tambaya shi ne ko me ya sa sarkin na Maroko ya ki amincewa ya tattauna da shugaba Jonathan ta wayar tarho, wasu dai na danganta hakan da yadda Najeriya ke dan nuna alamar goyon baya ga gwagwarmayar ballewa da al’ummar yankin Saharawiu a kungiyar Polisario ke yi daga Maroko, yayin da wasu ke cewa hakan ba ya rasa nasaba da kuri’ar goyon bayan Isra’ila a maimakon Palasdinu da Najeriya ta yi a kwamitin sulhu na Majalisar dunkin Duniya a shekarar da ta gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.