Tawagar Turai za ta ci gaba da sa ido a Najeriya
Tawagar masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za su ci gaba da zama a Najeriya har lokacin da za a gudanar da babban zabe a kasar. Kungiyar Kasashen Turai tace ta dauki zaben shugaban kasar Najeriya da za a yi a watan gobe da matukar muhimmanci saboda kimar kasar da farin jininta a duniya da kuma karfin tattalin arzikinta a Afirka.
Wallafawa ranar:
Shugaban tawagar masu sa ido na kungiyar Santiago Fisas ne ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso.
Jami'in ya ce zaben Najeriya na da matukar muhimmanci ga Afirka da kungiyar kasashen Turai.
Tawagar wakilan na Turai dai sun iso Najeriya tun kafin Jam'iyyun siyasa su yi taron zaben fidda gwani a tsakaninsu, kuma babban Jami’in na Turai ya ce suna nan suna ci gaba da sa ido kan abin da ke faruwa a Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu