Isa ga babban shafi
Faransa

Kasashen duniya su fito a yaki ta’addanci a Afrika- Hollande

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya yi kira ga kasashen duniya su fito su taimaka a kawo karshen ta’addanci a Afrika, yana mai cewa yakin ya fi karfin Faransa ita kadai. shugaban ya fadi haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a birnin Paris.

Shugaban Faransa Francois Hollande yana amsa tambayoyi a fadarsa Elysee a birnin Paris
Shugaban Faransa Francois Hollande yana amsa tambayoyi a fadarsa Elysee a birnin Paris Reuters
Talla

Kasar Faransa ta yanke shawarar taimakawa dakarun kasashen Chadi da Kamaru da Najeriya ta hanyar samar da makamai da sauran kayan aiki don fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram.

Tuni Tarayyar Afrika ta amince da tsarin kafa runduna ta kasashen biyar domin yakar Boko Haram da suka karbe ikon garuruwa da dama a arewa maso gabacin Najeriya.

Kasar Faransa yanzu haka nada dakaru dubu uku a yankin Sahel da nufin yaki da 'yan ta’adda, tare da bai wa dakarun Kamaru da Chadi bayanan sirri don yakar Boko haram.

“Faransa ba za ta iya kawo karshen rikicin kasashen duniya ba” a cewar Hollande.

Shugaban ya ce Faransa za ta bayar da taimakon makamai da bayanan sirri, tare da yin kira ga kasashen duniya su sani cewa taimaka wa ga yaki da ta'adanci hakkinsu ne.

Hare haren Boko Haram sun dagula zaman lafiya a iyakokin kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar. Hakan ya sa kasashen Chadi da Kamaru suka tura sojoji domin yakar Boko Haram a Najeiya.

A ranar Litinin ake sa ran Majalisar kasar Nijar za ta kada kuri’ar amincewa da matakin aikawa da dakaru domin yakar  Boko Haram.

Bako Haram dai ta karbe garuruwa da dama a yankin arewa maso gabacin Najeriya ciki har da garin Baga da ke kusa da tabkin Chadi magamar Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.

Tun 2009 da rikicin Boko Haram ya fara alkaluma na cewa mutane dubu goma sha uku aka kashe yayin da miliyan daya da rabi suka yi gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.