Shirin Dandalin Siyasa ya yi nazari ne game da 'Yan takarar da manyan Jam'iyyun siyasa a Najeriya suka tsayar domin wakiltarsu a babban zaben shekara mai zuwa. PDP mai mulki ta tabbatar da shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dantakarta, yayin da kuma APC mai adawa ta tsayar da Janar Muhammadu Buhari.