Isa ga babban shafi
Najeriya

An yankewa Soji 12 hukuncin kisa a Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta yankewa wasu sojojin kasar 12 hukuncin kisa saboda samun su da laifin budewa kwamnadansu wuta a Maiduguri a farkon wanna shekara

omg.com.ng
Talla

Sojin dai sun zargin kwamandan nasu ne da kin basu isassun kayan aiki da umurnin maida martani a lokacin da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram ke kai masu farmaki a fadan da suke da su a Maiduguri ta yankin Areawa maso gabashin Najeriya

Shugaban kotun sojin da ya saurari tuhumar da ake yiwa sojojin Brigediya Janar Chukwuemeka Okonkwo ya sanar da samun sojojin da laifin yin bore da kuma yunkurin kashe kwamandansu, Manjo Janar Garba Mohammed.

Kotun ta yankewa wani soja guda hukuncin daurin kwanaki 28 da aikin karfi.

A kwanan nan dai Soji a tarayyar Najeriya na ta fafatawa da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da aka bayyana na dada kama wurare da dama a jihar Borno da kuma wasu jihohin da ke makwabtaka da ita.

A kwanan nan ma Kungiyar Dattawa a Maiduguri ta koka akan cewar ga alamu Boko Haram na kokarin zagayesu, bayan da suka kama kauyuka da dama a zagayen Maiduguri a wani abin da wasu kafaifan watsa labarai suka kira da cewar Boko Haram ta yiwa Maiduguri kawanya.

Amma a zantawarsu da sashen hausa na rfi wasu daga cikin mazauna maiduguri sun bayyana cewar ba haka labarin yake ba, sai dai sun san da cewar Boko Haram sun kama kauyuka da dama a wajen birnin na Maiduguri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.