Isa ga babban shafi
Dandalin Siyasa

Dambarwar Siyasar Jam'iyyar PDP a Zamfara

Wallafawa ranar:

Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne akan dambarwar Siyasar shugabancin Jam'iyyar PDP da ke adawa a Jihar Zamfara, inda a A ranar 2 ga watan Satumba ne za'a gudanar da zaben shugabancin Jam'iyyar domin zaben wanda zai jagoranci Jam'iyyar wajen tunkarar Jam'iyya APC da ke mulki a Jihar a zaben 2015.

Tutar jama'iyar PDP mai mulki a Najeriya
Tutar jama'iyar PDP mai mulki a Najeriya
Talla

Yanzu dai Jam'iyyar ta PDP tana neman tsayayyen mutum mai jama'a da zai jagoranci Jam'iyyar ba tare da nuna son rai ba domin samun shugaban da zai jagoranci Jam'iyyar ga nasarar kawar da Jam'iyyar APC da ta kada su zabe a lokacin tana ANPP.

'Yan takara guda hudu ne dai ke neman shugabancin Jam'iyyar da suka hada da Alhaji Ibrahim Mallaha da ya jagoranci Jam'iyyar a lokacin da ta sha kaye a zaben 2011.

Akwai Alhaji Garba Kwaccido daya daga cikin Dattawan Jam'iyyar da suka dade suna adawa a tsohuwar PDP kafin shigowar tsohon gwamnan Jihar Mahmuda Aliyu Shinkafi.

Akwai kuma Senator Hassan Nasiha wanda ya sha kaye a lokacin da ya nemi yin tazarce karkashin inuwar PDP a zaben 2011 a mazabar Gusau da Tsafe.

Akwai kuma Aminu Koramar Boko Matashi daga cikin 'Yan takarar guda hudu wanda kuma ke da goyon matasan Jihar Zamfara.

Shirin ya tattauna da Dattawan Jam'iyyar ta PDP akan matsalolin da suka dabaibaye Jam'iyyar tare da zantawa da wadannan 'Yan takarar da neman jagorantar Jam'iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.