Shirin Dandalin Siyasa ya tattauna ne game da dambarwar Siyasar Jihar Adamawa a Najeriya inda 'Yan Majalisar Jihar suka tsige Gwamna Murtala Nyako da ke takun-saka da Shugaba Jonathan bayan gwamnan ya canza sheka daga Jam'iyyar PDP zuwa APC mai adawa.