Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan sandan Najeriya sun kwance bom a Abuja

‘Yan Sandan Najeriya sun ce sun yi nasarar dakile wani yunkurin kai wani harin bom da aka shirya kai wa cikin wata motar daukar Fasinja a Abuja, bayan sun yi amfani da na’urar binciken bom a tashohin shiga motocin haya.

'Yan Sandan Najeriya suna bincike a Abuja birnin Tarayya a inda aka kai harin Bom a Nyanya
'Yan Sandan Najeriya suna bincike a Abuja birnin Tarayya a inda aka kai harin Bom a Nyanya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Daga watan Afrilu zuwa yanzu an kai hare haren bama bamai guda uku a Abuja, hadi da mummunar harin da aka kai a tashar mota a Nyanya inda mutane 75 suka mutu.

Kakakin rundunar ‘Yan sanda Frank Mba yace wannan wani sabon salo nee da mahara suka fito da shi domin cusa shakku da fargaba a zukatan mutanen Abuja musamman baki.

Rundunar ‘Yan sanda ta yi kira ga shugabannin kungiyoyin motocin sufuri su gudanar da kwakkwaran bincike akan dukkanin Fasinjojin da ke shiga mota da kayayyakinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.