Isa ga babban shafi
Forbes

Putin ya kere Obama a jerin masu karfin fada aji a duniya

Mujallar Forbes da ke bayyana Mutanen da suka shahara ta fannin dukiya da iko a duniya tace Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya zarce Shugaban kasar Amurka Barack Obama wajen karfin ikon kujerarsa.

Shugaban Amurka Barack Obama yana gaisawa da shugaban Rasha Vladimir Poutine à garin Saint-Pétersbourg kasar Rasha
Shugaban Amurka Barack Obama yana gaisawa da shugaban Rasha Vladimir Poutine à garin Saint-Pétersbourg kasar Rasha REUTERS/Pablo Martinez Monsivais/Pool
Talla

A cewar Mujallar, Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya rikito kasa a kololuwar jerin Shugabannin duniya masu karfin iko, a karo na farko cikin shekaru uku, inda Shugaban kasar Rasha ya maye gurbinsa, a dai dai wannan lokaci da dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu ke tsami.

Shugaban Rasha da aka sake zabe bara yana rike da madafun ikon kasar ne na tsawon shekaru 13 yanzu.

Mujallar na cewa ta bangaren Shugaba Obama, abubuwan da suka yi masa cikas akwai yadda da jibin goshi ya tsallake takardamar da ta sarke game da kasafin kudi, lamarin da ya sa aka dakatar da harkokin Gwamnati na tsawon kwanaki 16.

A watan Agusta kasar Rasha ta samu galaba akan Amurka inda ta nuna jarumtaka wajen karban bakuncin tsohon jami’in leken asiri Edward Snowden wanda Amurka ke nema ruwa a jallo.

Haka kuma Mujallar tace Shugaban Rasha ya yi abin a jinjina masa wajen ganin Amurka bata kai wa Syria kazamin hari ba don ladabtar da Shugaba Bashar Assad.

Sauran wadanda suka zama jarumai a duniya a bana akwai Shugaban kasar China Xi Jinping, wanda ake sa ran zai kwashe shekaru yana shugabancin kasar.

Akwai Fafaroma Francis da ya zo na hudu, Ita kuma Shugaban Gwamnatin Jamus it ace Mujallar Forbe ta jera a matsayi na Biyar.

A Nahiyar Afrika wanda aka cinka wajen dukiya da iya tafiyar da harkoki kamfanoninsa shi ne Aliko Dangote na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.