Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen Turai sun janye haramcin shigar da makamai Syria

Kasashen Turai sun amince da matakin janye takunkumin shigar da makamai da suka kakabawa kasar Syria kamar yadda kasashen Birtaniya da Faransa suka bukata domin taimakawa ‘yan tawaye da makamai.

'Yan tawayen Syria
'Yan tawayen Syria www.ndtv.com
Talla

Sai dai kuma kasashen ba su fito sun bayyana lokacin da za su karfafawa ‘yan tawayen da makamai ba saboda gudun kada su keta yarjejeniyar da suka kulla tsakaninsu da Rasha da kuma Amurka ta zaman Lafiya

Bayan shafe sa’oi 12 ministocin harakokin wajen Turai na ganawa a Brussels, Sakataren harakokin wajen Birtaniya William Hague ya ce sauran takunkumin za su ci gaba da aiki akan gwamnatin Assad.

Kasashen Birtaniya da Faransa ne suka jagoranci dage takunkumin a yayin da kasashen Austria, Sweden, Finland da Jamhuriayr Czech bas u fito fili sun bayyana matsayarsu game da dage takunkumin ba.

“Aikawa da makamai, ya sabawa ka’idojin Nahiyra Turai, wanda yanki ne mai san zaman lafiya.” Inji Ministan harkokin wajen kasar Austria, Michael Spindelegger, wanda ya dade yana adawa da dage takunkumin.

Wata majiya daga ofishin hukokmomin Paris ta bayyana cewa dage takunkumin zai kasance ne kawai a rubuce domin ba za a aika da makaman ba sai nan da daya ga watan Agusta mai zuwa.

Rahotanni na nuna cewa, wannan mataki da kungiyar ta Turai ta dauka, na nuna cewa ya rage ga kowace kasa a nahiyar ta zabi yadda za ta aikawa da ‘yan tawayen makamai.

Ko da yake, Ministocin harkokin wajen kasashen Nahiyar na ikrarin cewa sun sha alwashin bin ka’idojin safarar makamai da dokar nahiyar ta gindaya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.