Isa ga babban shafi
India

Bukin Cika shekaru 100 da fara Nuna Fim a Indiya

A ranar 3 ga watan Mayu ne ma’aikatar Fina-finan ta Bollywood a India ta yi bukin cika shekaru 100 da fara nuna fim, kuma a bukin an fito da sabbin fina-finai guda biyu masu dauke da jigon waiwayen fina-finan Da da na zamani.

Rani Mukherjee, Tauraruwar Fim a Indiya
Rani Mukherjee, Tauraruwar Fim a Indiya Bollywood
Talla

Shekaru 100 ke nan da aka fara nuna Fim na indiya mai taken “Raja Harishchandra", a birnin Mumbai.

Akwai buki na musamman da sabbin wake kwake da aka fitar domin gudanar da bukin

Akwai dubban Fina-fiani da kuma kimanin tikitin shiga kwallon fina-finai Biliyan uku da ake sayarwa duk shekara a masana’antar Bollywood a India

Kuma masana’antar na samu ci gaba wajen samun kudaden shiga a Fina-finan da ake gabatarwa da harshen indiyanci.

04:03

Rahoto: Bukin cika Shekaru 100 da fara nuna Fim a Indiya

A baya dai Fina-finan da suka yi fice sun hada da Mehboob khan da Mother India a shekarun 1957 da suka shafi matsalolin India da ke dauke da rayuwa me ban tausayi.

A shekarun 1970 zuwa 1980 Fina-finan India sun sauya zuwa soyayya zalla da kuma Fim na fadace fadace wanda ya kara karfafa kasuwar fina finan.

A baya dai yana da wahala ayi sunbata a Fina-finan indiya sabanain yanzu da fina-finan Turawa suka tasiri a Fina-finan Indiya.

Fina-finan Indiya ba wai a indiya kawai suka yi fice ba, domin saboda ci gaban Bollywood a duniya ya sa wasu al’umomin kasashen duniya musamman Afrika suka lakanci harshen indiyanci, musamman a kasar hausa.

A Najeriya an samu wani Bakane, Aminu Abdullahi Ardo da ake kira Ameem khan wanda yanzu haka ake damawa da shi a harakar Fim a kasar india.

Ameen Khan yace ya haska a fina fina da dama da aka gabatar da harshen Talugu a kudancin Indiya. Kuma ya rera wakoki da harshen Indiyanci.
Ameen kahn

Hausawa dai suna ganin babu banbanci tsakanin al’adunsu da al’adun Indiya, kamar yadda Basira wata bakar Ba’indiya a Najeriya ke cewa saboda tasirin Fina-finan Indiya ya sa ake rawa da waka a Fina-Finan Hausa.

Akwai sabon Fim da aka kaddamar na musamman game da bukin cika shekaru 100 na bollywood mai taken Bombay Talkies kuma Fim din ya kunshi fitatttun taurari da suka hada da Nawazuddin Siddiqui da Rani Mukherjee, da Amitabh Bachchan da Aamir Khan da Shah Rukh Khan, da Priyanka Chopra da kuma Kareena Kapoor. Wanda Karan Johar ya jagoranta kuma mai dauke da zubin wakokin iri daban daban.

An kiyasata masana’antar Bollywood za ta samu ci gaba wajen samun kudaden shiga nan da shekaru biyar masu zuwa daga kudi Dalar Amurka Biliyan Biyu zuwa Dala Biliyan uku da Miliyan Shida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.