Isa ga babban shafi
Najeriya-Holland

Kotu ta yi watsi da koken wasu Manoman Najeriya akan Shell

Wata kotu da ke Hague na kasar Netherlands ta yi watsi da karar da wasu mazauna yankin da ake hakan albarkatun man fetur a Najeriya suka shigar domin kalubalantar Babban Kamfanin hako Mai na Shell saboda gurbata ma su gonaki.

Jahar Bayelsa a yankin Neja Delta a Najeriya.
Jahar Bayelsa a yankin Neja Delta a Najeriya. REUTERS/Akintunde Akinleye /Files
Talla

Kotun ta tsame hannun Reshen babban kamfanin na Shell daga dukkan zargi da ake yi wa reshensa da ke Najeriya.

Manoma hudu ne tare da goyon bayan wasu kungiyoyi da abokansu, suka fara shigar da kara domin kalubalantar Kamfanin Shell a gaban kotu a 2008, inda suke zargin kamfanin da gurbata ma su muhalli.

Kotun tace kamfanin Shell zai biya diyya ne kawai ga manoma da masunta a daya daga cikin dimbin wuraren da ake neman diyya daga kamfanin da ke kauyen Ikot Ada Udo da aka sami wani rijiyan mai yana tumbudi.

Manoman da masuntan sun ce za su daukaka kara game da wannan hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.