Isa ga babban shafi
Najeriya

Hankula sun kwanta a rikicin Fulani da Gwarawa a Najeriya

A Nigeria, hankula sun fara kwanciya, a babban birnnin kasar Abuja, bayan da wani rikici tsakanin Fulani da al’ummar gwarawa, ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 2, tare da raunata wasu dadama.

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

An sami kwantar da tarzomar, da ta yi sanadiyar mutane 1,500 suka rasa gidajen su, ne bayan da hukumomin yankin na Abuja da hukumar agajin gaggawan kasar ta NEMA, suka shiga tsakani.
 

Daya daga cikin shugabannin Fulanin kasar, Alhaji Muhammad Dodo Oroji, ya nemi a gudanar da bincike kan lamarin, tare da hukunta masu hannu cikin lamarin, don kaucewa sake faruwar irin hakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.