Isa ga babban shafi
Lagos

An bude Wasannin kasa na Najeriya a Legas

An Bude Wasannin kasa a birnin Lagos karo na 18. Wasannin da kuma za su hada ‘yan wasa daga Jahohin kasar 36 hadi da birnin Tarayya Abuja. Akwai wasanni sama da 20 da za’a gudanar da suka hada da wasannin gargajiya irinsu Dambe da Langa da kuma Kokuwa.

Tawagar Lagos a ranar bukin bude wasannin kasa na Najeriya
Tawagar Lagos a ranar bukin bude wasannin kasa na Najeriya Giantcomfort
Talla

An dai fara gudanar da Wasannin ne a shekarar 1973 bayan kammala yakin Basasa.

A lokacin da yake jawabi Mataimkin Shugaban kasa Namadi Samob yace ana shirya gudanar da wasannin ne don kara hada kan ‘yan kasa da inganta zaman lafiya tsakanin kabilun Najeriya ta hanyar Wasanni.

Gwamnan Legas Babatunde Raji Fashola yace yana fatar a gudanar da wasannin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba kamar yadda aka gudanar da wasannin a Jahohin Ogun da Kaduna da kuma Rivers.

Za’a dai kwashe tsawon mako biyu ana gudanar da wasannin kuma akwai kyautaka da dama za’a ba ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.