Gwamnatin Bauchi ta kafa kwamitin sasanta rikicin Tafawa Balewa a Najeriya
A Najeriya mako daya bayan canja mazaunin karamar hukumar Tafawa Balewa, zuwa garin Bununu, gwamnatin Jahar Bauchi ta bullo da wani zauren tuntuba da yafewa juna tsakanin kabilun da ke fafatawa da juna a wannan yanki.
Wallafawa ranar:
Rehoton Shehu Saulawa Daga Bauchi
Mai Martaba Sarkin Bachi Alh. Rilwanu Sulaiman Adamu wanda shi ne shugaban zauren muhawarar yace babban aikin da ke gabasu shi ne tattaro bayanai daga kabilun da rikicin ya shafa domin yafewa wa Juna tare da ba gwamnatin Shawara.
An kwashe sama da shekaru 40 ana fafata tsakanin kabilun Fulani da Sayawa kan mallaka amma ana tunanin zauren sasantawar zai shawo kan matsalar tsakanin kabilun biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu