Isa ga babban shafi
China-Lafiya

Coronavirus babbar barazana ce ga duniya baki daya- WHO

Adadin mutanen da cutar coronavirus ta kashe a China ya haura dubu guda dai dai lokacin da hukumar lafiya ta duniya WHO ke gargadi kan yadda annobar cutar ta zama babbar barazana ga duniya baki daya.

Jami'an kula da masu dauke da cutar Corona a yankin Wuhan na China.
Jami'an kula da masu dauke da cutar Corona a yankin Wuhan na China. REUTERS/Adriano Machado
Talla

Yayin taron WHO yau Talata a Geneva bayan karuwar adadin da ke dauke da cutar a China dama ci gaba da fantsamarta sauran kasashen duniya, WHO ta bayyana cutar ta corona a matsayin babbar barazana ga duniya baki daya.

Taron na WHO na zuwa dai dai lokacin da China ke karfafa matakan yaki da cutar da yanzu haka ta kama fiye da mutane dubu 42, baya ga yaduwarta kasashe 25,inda ko a yau aka samu rahoton mutuwar mutum 108.

A cewar Tedros Adhanom Ghebreyesus shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, China ke da kashi 99 na cutar ta corona matakin da ke nuna bukatar agajin da kasar ke yi.

Miliyoyin mutane ne dai mahukuntan na China suka kulle a mabambantan birane don gudun yaduwar cutar, matakin da WHO ke cewa akwai tsananin bukatar agajin gaggawa.

Bayan matakin kasashe na hana safarar jiragensu zuwa China da kuma tantancewa kafin karbar bakin da suka iso daga Chinar kamuwar dan birtaniya guda da ya shafawa mutane 11 cutar ta Corona ba kuma tare da ya ziyarci China ko ya yi mu’amala da wani da ya zo daga kasar ba, ya matukar tayar da hankali tare da raba tunanin masana kan ko wani nau’in cutar na shirin barkewa a Turai.

Yanzu haka Japan na da mutane 135 da suka kamu da coronavirus yayinda ko a yau Talata, aka kwashe fiye da mutane 100 daga wani dogon gini mai hawa 35 da ke dauke da mutane fiye da dubu 3, bayan gwajin wasu mutum 2 da aka gano suna dauke da cutar a Hong Kong, inda dukkanninsu za su fuskanci gwaje-gwajen lafiya don gudun fantsamar cutar zuwa wasu sassa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.