Isa ga babban shafi
Lafiya

Afrika ta Kudu ta samar da maganin Kanjamau

Afrika ta Kudu ta ce, za ta kaddamar da maganin Kanjamau na zamani kuma mai rahusa domin yaki da cutar a tsakanin dimbin al’ummar kasar da ke fama da ita.

Maganin Dolutegravir  na da tasiri wajen magance cutar Kanjamau
Maganin Dolutegravir na da tasiri wajen magance cutar Kanjamau nation.co.ke
Talla

Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Afrika ta Kudu ta ce, za a fara kaddamar da kwayoyin maganin mai suna TLD a ranar 1 ga watan Disamba, wato ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da cutar kanjamau.

Ministan Lafiyar kasar, Zweli Mkhize ya kaddamar da samfaurin maganin a wani biki da ya gudana a yamma maso kudancin lardin KwaZulu-Natal, wato yankin da ya fi yawan masu dauke da cutar ta Kanjamau a kasar.

An samar da maganin mai dauke da nau’ukan sinadarai uku tare da tallafin Kungiyar Bunkasa Kiwon Lafiya ta Duniya.

Daga cikin sinadaran har da Dolutegravir wanda Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a matsayin sinadarin maganin da ke kan gaba wajen yaki da cutar.

Darektan Kungiyar Bunkasa Lafiyar ta Duniya, Robert Matiru ya ce, sabon maganin na TLD na da tasiri matuka, kuma yana murkushe kwayoyin cutar cikin gaggawa fiye da maganin da ake amfani da shi a yanzu haka.

Afrika ta Kudu dai, nada sama da kashi 10 daga cikin jumullar alkaluman mutane da ke mutuwa a sanadiyar cutar HIV, yayin da kuma take da kashi 15 na jumullar sabbin mutanen da ke kamuwa da ita .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.